Abu takwas game da Abba Kabir Yusuf zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano
A ranar litinin ne hukumar zaɓe mai zaman kanta ta sanar da Abba Kabir Yusuf wanda ake yi wa laƙabi da Abba gida-gida a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano.
Ga abu takwas da ya kamata ku sani a kansa:
- An haife shi ranar 5 ga watan January, 1963 a ƙaramar hukumar Gaya ta jihar Kano.
- Ya yi karatun Firamare a makarantar gwamnati da ke Sumaila Primary School sannan kuma ya yi karatun Sakandire a makarantar gwamnati ta Lautai a Gumel da ke jihar Jigawa.
- Abba ya yi karatun difloma a kwalejin kimiya da fasaha ta Mubi sai kuma babbar difloma a kwalejin kimiya da fasaha ta Kaduna watau Kaduna Polytechnic.
- Ya yi karatun digirinsa na biyu digiri a jam’iyyar Bayero ta Kano a fannin harkokin kasuwanci.
- Tsohon kwamishinan ayyuka a jihar Kano a zamanin mulkin Rabi'u Musa Kwankwaso.
- Abba gida-gida ya yi takarar gwamna a jam’iyyar PDP a jihar Kano a shekarar 2019 amma bai samu nasara ba.
- Yana da mata biyu da ‘ya’ya da dama.
- Ya lashe zaɓen gwamnan jihar Kano a ranar 20 ga watan Maris na 2023.
