/> An Yanke Wa Mujra Ibrahim Hukuncin Sharar Asibitin Murtala, Kano - Arewa24
Lorem ipsum dolor sit amet, consectetur adipiscing elit. Test link
AGCYSWP78
Posts

An Yanke Wa Mujra Ibrahim Hukuncin Sharar Asibitin Murtala, Kano

 








Babbar kotun shari'ar Musulunci da ke Hausawa Filin Mushe a Kano ya yanke wa Jarumar TikTok din nan, Murja Ibrahim Kunya hukuncin sharar masallaci. 


Kotu da ke karkashin jagorancin Mai Sharia Abdullahi Halliru, ta yanke wa sauran abokan burmin nata hukunci makamancin wannan. 


A hukuncin da kotun ta yanke yau Juma'a, ta bukaci Murja Ibrahim ta rika sharar Asibitin Murtala na tsawon sati uku, sannan za ta dinga zuwa Hisba tsawon watanni shida daga ranar Litinin zuwa Alhamis.


Kodayake hukuncin bai fayyace ko za a dinka wa Murja Ibrahim kayan Hizba ba ne, amma dai kotun ta bukaci za ta rika zuwa tun daga karfe 8-5 na kowace rana, tare da yi mata wa'azi don a tabbatar ta natsu. 


Su kuwa Aminu BBC da Ashiru Idris Mai Wushirya da Sadik Sharif za su dinga sharar Masallacin Murtala har tsawon sati uku.


Wadannan kotun ta yanke wa hukunci ta tura su zaman wakafin na tsawon makonni bayan karar da zauren malaman Kano ta shigar a kan matasan saboda wallafa bidiyon badala a TikTok.

Da yake yi wa manema labarai karin bayanin bayan an fito daga zaman kotun, mai gabatar ta kara Lamido Abba Sorondinki, ya tabbatar da cewa an samu Sadik Sharif Umar da yin wasu wakoki masu dauke da kalaman batsa da lalata tarbiyyar yara.


Kotun ta bukaci Lauyan gwamnati da sauran jami'an Hisba su tabbatar wadanda aka yanke wa hukuncin sun bi shi sau da kafa, idan kuma sun saba za a iya koma wa kotu a sake sabon lale.


JARIDAR AMANA ta fahimci sai da masu gabatar da kara suka janye wasu tuhume-tuhume guda biyu da ake yi wa Murja Ibrahim kafin suka samu sassauci a wannan hukuncin sakamakon yarjejeniyar da aka yi da ita na bin hukuncin sau da kafa.

L