Zaɓen Najeriya 2023: Sakamakon zaɓen gwamnan jihar Kaduna
Wasu yan takarar gwamnan jihar Kaduna
A ranar 18 ga watan Janairu ne al'ummar Najeriya ke gudanar da zaɓen gwamnoni a jihohi 28, da kuma na majalisar dokokin jiha a faɗin ƙasar.
Kaduna ce jiha ta uku mafi yawan al'umma a Najeriya. Alƙaluman hukumar zaɓen ƙasar sun nuna jihar cewa na da masu rijistar zaɓe 4,335,208.
Jihar na da yawan ƙananan hukumomi 23.
Ƴan takara 14 ne ke neman maye gurbin gwamna El-Rufai a zaɓen da ke tafe.
