Sakamakon zaben gwamnan Kano ya fara isowa
Hukumar zaɓen Najeriya INEC ta fara bayyana sakamakon zaɓen gwamna na jihar Kano dake arewa maso yammacin Najeriya, da aka gudanar ranar Asabar.
Hukumar zaben ta fara karɓar sakamakon ne da misalin karfe uku na yammacin Lahadi.
Fafatawar dai ta fi zafi ne tsakanin jam'iyyar APC mai mulkin jihar da kuma jam'iyyar NNPP babbar mai hamayya da PDP.
Jam'iyyar NNP ce ta lashe zaɓen shugaban ƙasa da kujeru biyu na sanatoci uku dake jihar, da kuma mafi yawan kujerun majaliasar wakilan tarayya daga jihar.
Jihar Kano na da ƙananan hukumomi 44.
Karamar hukumar Rano
APC 17,090
NNPP 18,040
PDP 225
ADP 92
Ƙaramar hukumar Rogo
APC 11,112
NNPP 18,559
PDP 124
ADP 42
Ƙaramar hukumar Makoda
APC 15,006
NNPP 13,956
PDP 101
ADP 83
Ƙaramar hukumar Ƙunchi
APC 13,215
NNPP 10,674
ADP 62
PDP 39
Za mu ci gaba da kawo muku sakamako daga sauran ƙananan hukumomin da INEC ta sanar.
