Kamar yadda mu ka ambata tun da farko duk mai fama da daya ko wasu daga matsalolin can da mu ka zana a sama magance su shine warakarsa da ikon Allah. Duk da haka Hausawa kan ce, idan kana da kyau ka kara da wanka bayan magance kalubalen lafiya da ake fama da ita/su za a iya amfani da wadannan hade-hade da zamu zana a kasa.
Hakanan, ko da mutum ba ya fama da daya daga cikin wadancan matsaloli, masana na ba da shwarar yawaita motsa jiki da kuma lura da nau'in abincin da ake ci. Domin samun cikakken bayani karanta makalarmu mai kanun "Nau'ikan Abinci Ma Su Karawa Namiji Sha'awa Da Kuzari Yayin Jima'i" Da kuma "Nau'ikan Abinci Ma Su ragewa Ma'aurata Sha'awa Yayin Jima'i" za su taimaka ma ka kwarai gaya.
