Zaɓen Najeriya 2023: Sakamakon zaɓen gwamnan jihar Kano
Wasu ƴan takarar gwamnan jihar Kano
A ranar 18 ga watan Janairu ne al'ummar Najeriya ke gudanar da zaɓen gwamnoni a jihohi 28, da kuma na majalisar dokokin jiha a faɗin ƙasar.
Kano ce jiha ta biyu a yawan masu rajistar zaɓe a Najeriya. Alƙaluman hukumar zaɓen ƙasar sun nuna jihar tana da masu rijistar zaɓe 5,921,370.
Akwai ƴan takarar wannan kujera ta gwamnan jihar Kano har 17 a zaɓen mai zuwa, wanda za a yi lokaci ɗaya da na ƴan majalisar dokoki.
Jihar na da yawan ƙananan hukumomi 44.
