Hotunan yadda ƴan sandan Isra'ila suka kai samame kan masallata a Masallacin Kudus
Ƴan sandan Isra'ilan sun kai samame Masallacin Kudus ɗin ne lokacin da musulmi ke ibada.
Ƴan sandan sun ce sun kai harin ne a matsayin martani ga masu zanga-zanga.
Kakakin shugaban Falasɗinawa ya yi Allah-wadai da harin na Isra'ila, yana cewa da ma sun gargaɗi masu mamayen kada su keta haddin wurin, ta hanyar shiga wuraren ibada masu tsarki na Masallacin, abin da zai iya haddasa mummunan rikici.



