/> TIRKASHI: ‘Yan sanda sun kama wasu da ake zargin suna da hannu wajen kashe dalibar da tai batanci ga Annabi Muhammad - Arewa24
Lorem ipsum dolor sit amet, consectetur adipiscing elit. Test link
AGCYSWP78
Posts

TIRKASHI: ‘Yan sanda sun kama wasu da ake zargin suna da hannu wajen kashe dalibar da tai batanci ga Annabi Muhammad

 








TIRKASHI: ‘Yan sanda sun kama wasu da ake zargin suna da hannu wajen kashe dalibar da tai batanci ga Annabi Muhammad


Wannan na Zuwane bayan kashe tareda kona wata daliba a kwalejin jahar sokoto kan batanci ga Annabi Muhammad s.a.w


Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Sokoto, ta tabbatar da cafke wasu dalibai biyu da ake zargi da hannu a kisan gilla da aka yi wa wata daliba mai suna Deborah Samuel bisa zargin yin batanci a jihar.

A cewar PRO, an kama dalibai biyu da laifin hadabaki kan lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar Deborah.


Kafin rasuwarta, Deborah daliba ce a mataki na biyu a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagiri, Sokoto.


An zarge ta da yin kalamai marasa dadi game da Annabi Muhammad (Amincin Allah ya tabbata a kareshi) a harabar jami’ar kuma nan take aka yi mata barazana ga lafiyarta.


Daga nan aka kai ta ofishin jami’an tsaro na makarantar domin tsira. Sai dai ‘yan zanga-zangar sun bi ta har zuwa ofishin jami’an tsaro inda suka yi galaba a kan ma’aikatan.

Anan ne aka kashe ta kamar yadda wasu faifan bidiyo da ke yawo a yanar gizo suka nuna.


Rundunar ‘yan sandan jihar bayan da ta kwantar da tarzoma, ta yi kira ga jama’a da su ci gaba da gudanar da ayyukansu, kuma kada su firgita saboda halin da ake ciki.


“Bayan samun labarin, rundunar ‘yan sandan DC Operations ta jagoranci tawagar ‘yan sanda da dukkan sauran kwamandojin gudanarwa na jihar zuwa makarantar, An kama dalibai biyu.


Hukumomin makarantar sun rufe makarantar, kuma an tura ‘yan sanda domin bayar da tsauraran matakan tsaro.

“Kwamishanan ‘yan sanda reshen jihar Sokoto, Kamaldeen Kola Okunlola, yana kira ga jama’a da su gudanar da ayyukansu, kuma kada su firgita saboda halin da ake ciki. A halin da ake ciki, an kuma ga wadanda ake zargin a cikin faifan bidiyo da aka yada a Twitter kuma za a yi musu bincike nan ba da dadewa ba,” in ji sanarwar ‘yan sandan.

L