/> An kashe sojojin Isra'ila uku a kusa da kan iyakar Masar - Arewa24
Lorem ipsum dolor sit amet, consectetur adipiscing elit. Test link
AGCYSWP78

An kashe sojojin Isra'ila uku a kusa da kan iyakar Masar

 







An kashe sojojin Isra'ila uku a kusa da kan iyakar Masar




Rundunar sojin Isra'ila ta ce dakarun sojin Masar sun halaka sojojinta uku a kusa da kan iyakar ƙasashen biyu.


An dai tsinci gawarwakin sojojin a kusa da kan iyakar ƙasar da safiyar ranar ranar Asabar, bayan da aka kasa samunsu a waya


Rundunar sojin Isra'ila ta ce za ta gudanar da bincike tare da haɗin gwiwwar dakarun sojin Masar.


Sojojin na Isra'ila sun ce an tsinci gawarwarkin sojojin sa'o'i bayan wani farmaki kan masu safarar ƙwaya a kan iyakar ƙasashen.


Mai magana da yawun rundunar Sojin Isra'ila ya ce an ƙwace miyagun ƙwayoyi da kudinsu ya kai 400,000 daga hannun wani da ya yi yunƙurin tsallaka kan iyakar ƙasar.


Ya ce suna zargin kisan sojojin na da alaƙa da farmaki kan masu safarar ƙwayar.


Ana dai yawan samun arangama tsakanin dakarun sojin Isra'ila da masu safarar ƙwayoyi da ke yunƙurin shigar da ƙwaya ta kan iyakar ƙasashen biyu.



L