/> Gwamnan Kano ya nada Akanta-Janar da wasu shugabannin hukumomi 4 - Arewa24
Lorem ipsum dolor sit amet, consectetur adipiscing elit. Test link
AGCYSWP78
Posts

Gwamnan Kano ya nada Akanta-Janar da wasu shugabannin hukumomi 4

 



Gwamnan Kano ya nada Akanta-Janar da wasu shugabannin hukumomi 4



Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya nada Abdulkadir Abdussalam a matsayin sabon Akanta Janar na jihar.


Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya fitar jiya.


Ya ce Gwamnan ya kuma nada Garba Ahmed-Bichi a matsayin sabon Manajan Daraktan Hukumar Ruwa ta Jihar Kano.


A cewar sanarwar, Yusuf ya nada Dakta Rahila Mukhtar a matsayin Babban Sakatariyar Hukumar Kula da Gudunmawar Kiwon Lafiya ta Jihar Kano, KCHMA.


Hassan Baba Danbaffa kuma an nada shi a matsayin Manajan Darakta na Hukumar Kula da Tituna ta Jihar Kano, KARMA.


Gwamnan ya kuma nada Arc. Ibrahim Yakubu, a matsayin Manajan Daraktan Hukumar Tsare-Tsare da Cigaban Birane ta Jihar Kano, KNUPDA.


Dawakin-Tofa ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba za a sanar da bikin rantsar da wadanda aka nada domin samun damar karbar ragamar aiki nan take.



L