/> Mutane da dama sun jikkata bayan hatsarin jirgin ƙasa a Indiya - Arewa24
Lorem ipsum dolor sit amet, consectetur adipiscing elit. Test link
AGCYSWP78
Posts

Mutane da dama sun jikkata bayan hatsarin jirgin ƙasa a Indiya

 



Mutane da dama sun jikkata bayan hatsarin jirgin ƙasa a Indiya


Akalla mutum 100 ne aka bayar da rahoton sun jikkata bayan wasu jiragen kasa guda biyu sun yi taho-mu-gama a jihar Odisha da ke gabashin kasar Indiya.


Kusan motocin daukar marasa lafiya 50 ne aka aika zuwa wurin da lamarin ya faru a Lardin Balasore, a cewar babban sakataren jihar.


Ana kuma fargabar cewa mutane da dama sun rasa ransu.


Firaministan Indiya Narendra Modi ya wallafa a shafinsa na Twitter inda yake cewa yana cikin matukar damuwa sakamakon hadarin kuma ya na taya wadanda suka rasa 'yanuwansu jimamin rashin.


Taragan jirgi da dama ne suka kauce daga layin dogo.



L