/> YANZU-YANZU: Tinubu ya yi sabbin naɗe-naɗen muƙamai - Arewa24
Lorem ipsum dolor sit amet, consectetur adipiscing elit. Test link
AGCYSWP78
Posts

YANZU-YANZU: Tinubu ya yi sabbin naɗe-naɗen muƙamai

 



YANZU-YANZU: Tinubu ya yi sabbin naɗe-naɗen muƙamai


Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da sabbin nade-nade kwanaki kadan bayan rantsar da shi.


Femi Gbajabiamila, kakakin majalisar wakilai shi ne sabon shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, yayin da Ibrahim Hadejia wanda tsohon mataimakin gwamnan jihar Jigawa ne ya zama mataimakin shugaban ma’aikata.


Abiodun Oladunjoye, Daraktan Yada Labarai na ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai ne ya bayyana hakan a yau Juma’a a Abuja.


Ya ce shugaban ya kuma nada George Akume, tsohon gwamnan Benue a matsayin sakataren gwamnatin tarayya, SGF.



L