Jaridar Labaran Hausa ta ruwaito cewa.
Rundunar ‘yan sanda a birnin Riyadh ta tabbatar da kama wani mutumi wanda ya zagi Sayyada Aisha R.A, matar Annabi Muhammad (SAW).
Manjo Khaled Al-kraidis, wanda yanke shine kakakin rundunar ‘yan sandan Riyadh, ya bayyana cewa a wani bidiyo da aka wallafa a shafukan sadarwa, an gano cewa bidiyon cin mutuncin ne ga Annabi Muhammad (SAW), haka kuma zagi ne ga uwar muminai, Aisha (R.A).
Bayan kama mutumin an gabatar dashi a gaban kotu domin yanke masa hukumcin daya dace da shi.
An wallafa bidiyon ne a shafukan sadarwa a ranar 10 ga watan Muharram, a lokacin da ‘yan kungiyar Shia suke nuna bakin cikinsu kan kisan da aka yiwa Sayyadina Hussain a lokacin yakin Karbala.
A Musulunci, duka matan Annabi Muhammad guda 11 ana daukar su a matsayin iyaye a Musulunci, a ka’ida ma Musulmai suna so da kuma girmama su fiye da iyayen da suka haife su.
