/> Anyi wa shugaban Facebook tiy*ata yanzu haka yana kwa*nce a Asibiti ...shine mamallakin Instagram da WhatsApp Ku latsa hoton dake kasa domin karanta cikakken labarin ⤵️ - Arewa24
Lorem ipsum dolor sit amet, consectetur adipiscing elit. Test link
AGCYSWP78
Posts

Anyi wa shugaban Facebook tiy*ata yanzu haka yana kwa*nce a Asibiti ...shine mamallakin Instagram da WhatsApp Ku latsa hoton dake kasa domin karanta cikakken labarin ⤵️




An yi wa mamallakin Facebook wanda ya kafa kamfanin Meta, Mark Zuckerberg tiyata bayan ya samu rauni a gwiwarsa a lokacin da ya ke atisaye don shiga a fafata dashi a gasar kokowa da za ayi a farkon baɗi 2024.


A wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Instagram a ranar Juma’a, Zuckerberg ya bayyana cewa ya samu tsagewar ƙashi a guiwa amma dai anyi masa tiyata kuma yana samun sauƙi.


Wakiliya ta ruwaito shugaban kamfanin Meta din wanda kuma shine kamfanin da ya mallaki Facebook, da Instagram da WhatsApp yana cewa, “Ina kan murmurewa kuma na gode wa tawagar likitoci da ke kula da ni.


“Har yanzu ina fatan shiga gasar kokowar amma sai bayan na warke.”


“Na gode wa kowa da kowa da suka nuna mini ƙauna da goyon baya a wannan lokaci.”


Dan shekaru 39 din ya kuma wallafa jerin hotuna da ke nuna shi a gadon asibiti.




L